Kungiyar kwallon kafa Juventus ta yi watsi da tayin fam miliyan 86 da Liverpool ta yi wa Dan wasan ta Federico Chiesa. Dan wasan gaban na gefe mai shekara 23, ya taka wa Italiya leda a gasar cin kofin Turai da aka yi a kwana kwanan wato Euro 2020. Jaridar Repubblica.
kungiyar Arsenal da da takwarar ta Tottenham da kuma Everton, dukkaninsu na duba yuwuwar zawarcin dan gaban Argentina Joaquin Correa, mai shekara 26,wanda ake sa ran zai bar Lazio a bazaran nan. Inji jaridar (Corriere dello Sport)
KARANTA WANNAN LABARIN: Manoman Jigawa Sun Sami tallafin aikin N10b
Watakila kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nemi sayar da Anthony Martial, mai shekara 25, da Tottenham ke sha’awar dan gaban dan Faransa. Kamar yaddaJaridar Star ta ruwaito.
Kazalika Shi kuwa Mai horas da United Ole Gunnar Solskjaer ya na son Paul Pogba, mai shekara 28, ya cigaba da zama a kungiyar a, ya yin da kungiyar Paris St-Germain dake Faransa, ke son dan wasan tsakiyar da ya dawo faransa. Inji jaridar (Manchester Evening News)
Arsenal na fatan tabbatar da sayen dan bayan Brighton, dan kasar Ingila Ben White mai shekara 23, a kan fam miliyan 50, bayan kammala gwajin lafiyarsa a karshen makon nan. (Jaridar Mail)
A karshe Gunners din na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya dan Switzerland Denis Zakaria, mai shekara 24, wanda ya bayyana aniyarsa ta barin Borussia Monchengladbach. (Jaridar Mirror)