- Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya roki shugabannin NLC da kada su tafi yajin aiki.
- Ndume ya roki shugabannin kungiyar NLC da su shiga tattaunawa a matsayin wata hanya ta daidaita lamarin.
- Ndume yayi kira ga shugaban kasa Tinubu, da ya gana da shugabannin kungiyar kwadago da kan sa.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, APC, Borno ta Kudu, ya roki shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC da su janye yajin aikin da ake sa ran za a fara ranar Laraba mai zuwa,Vanguard ta rawaito.
Ndume wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin soji ya roki shugabannin kungiyar NLC da su shiga tattaunawa a matsayin wata hanya ta daidaita lamarin, inda ake samun rashin fahimtar juna tsakanin hukumar da gwamnatin tarayya kafin fara yajin aikin.
KARANTA WANNAN: Otti Ya Umurci Jami’an Gwamnatin Data Shude Su Maido Da Kadarorin Gwamnati
A wata sanarwa daya fitar jiya a Abuja Ndume wanda shine Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, yayi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya gana da shugabannin kungiyar kwadago da kan sa ya kuma basu tabbacin alfanun cire tallafin man fetur.
Ya ce, “Wannan cire tallafin man fetur abu ne da ya kamata mu yi a yanzu ko kuma ba za mu taba yi ba,” in ji shi.
“Muna bukatar mu bude raunukan a yanzu mu fara warkar da su. Akwai bukatar kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta hada kai da gwamnati domin ganin yadda za a rage illar.
“Idan har yanzu ba mu cire tallafin ba, wasu za su ci gaba da shan nonon kasar nan. Ya kamata NLC ta hau teburin tattaunawa da Gwamnatin Tarayya.”
“Kada NLC ta fara yajin aikin kafin a tattauna. Kada su yi wannan kuskuren. Bayan haka, babu kasafin kudin tallafin. Daga ina kudin zasu fito?
“Ina kira ga shugaba Tinubu da ya gana da shugabannin kungiyar kwadago da kan sa ya warware matsalolin. Ya kuma tabbatar musu da cewa al’amura za su daidaita”.
A wani labarin kuma, Abubuwa Biyar Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cire Tallafin Man Fetur
Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu a jawabinsa na farko ya sanar da cire tallafin man fetur.
Da wannan sanarwar, farashin PMS da aka fi sani da man fetur ya yi tashin gwauron zabbi inda ake cefanar dashi kusa naira 700 kan kowacce Lita.
Kwanaki biyu bayan da Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur NNPCL ya kara farashin Famfo na man Fetur