Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai wa ayarin motocin matr gwamnan jihar Osun, Misis Kafayat Oyetola hari da yammacin ranar Juma’a.
Duk da cewa har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto ba a samu cikakkun bayaniai kan lamarin, Amma wata majiya daga garin Owode, Ede, inda lamarin ya faru, ta ce ayarin motocin Misis Oyetola na kan hanyar zuwa Osogbo kuma suna kusa da kasuwar Owode ne aka ji karar harbe-harbe da misalin karfe 8 ranar Juma’a.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa amma aka bayyana shi da Alayande, ya shaida wa wakilin Jaridar PUNCH a ranar Asabar cewa wata babbar mota ce ta kawo cikas a tafiyar ayarin motocin inda aka samu cunkoson ababen hawa a lokacin da ayarin motocin suka isa mahadar kasuwar Owode.
“A lokacin da ake kokarin sa direban babbar motar ya matsa ne aka samu sabani tsakanin jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin.
“Na ji karar harbe-harbe da dama inda na tsaya kusa da mahadar motoci. Ga shi duhu ne amma an samu sabani tsakanin jami’an tsaro da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne,” inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, bai mayar da martani ga sakon kartak kwana da aka aike masa kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Sai dai jami’ar yada labarai na ofishin uwargidan gwamnan jihar Oluwatunmise Iluyomade ta ce an kai wa ayarin motocin hari.
Ta ce “Babu wani rai da aka rasa a lamarin. Amma Wasu jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin sun samu raunuka daban-daban.”