Gwamnatin jihar Kano ta fitar da takadar sanarwa, wanda gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje ya bada sanarwar za a yi sallar Idi a jihar.
Gwamna Ganduje ya bada sanarwar ne jim kadan bayan biyo karin sati biyu da Kwamitin kar-ta-kwana na shugaban kasa kan annobar COVID19 ta kara.
A sanarwar an gwamnatin ta sake yin duba ga dokar kullen tare yin sauye-sauye kamar haka:
i) An sauya dokar daga awanni 16 zuwa awanni 18 kuma za ake sakin gari a ranakun Litinin, Laraba da kuma ranar Juma’a daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.
ii) Gwamnatin ta umarci hukumar Hisbah da ta tura jami’anta masallatan juma’ah domin tabbatar da cewa jama’a sun bi dokar bada kariya da kuma tazara.
iii) Gwamnatin Kano zata bari a yi sallar idi a dukkanin masarautu biyar da ake da su a jihar cikin tsari da bin doka.
iv) Har wa yau, gwamnatin ta ce babu wasu bukukuwan sallah da za a gudanar a jihar wanda ya hada da bikin hawan sallah da aka saba duk shekara.
v) Gwamnatin ta yi alkawarin cigaba da ba da kariya ga al’ummar jihar tare da neman hadin kansu domin kawo karshen wannan annoba ta corona virus.
Daga: Abubakar Muhammad Usman