Manajan kungiyar kwallon kafa ta Everton dake ƙasar Ingila Carlo Ancelotti ya yi bankwana da kungiyar inda ya koma tsohuwar zuma Real Madrid ta kasar Spaniya a karo na biyu.
Anceloti mai shekara 61 daya wanda dan asalin kasar Italiya ne, ya bar Everton ne bayan da ya shafe watanni 18 yana horas da kungiyar.
A baya dai kocin ya taɓa rike Madrid na tsawon shekara biyu, daga 2013 zuwa 2015.
Bankwana da ya yi da Everton don maye gurbin Zidane ya sa ala tilas Ƙungiyar za ta bazama kasuwa kenan don samun gurbinsa.
Anceloti ya sanya hannu ne kan kwantiragin shekara uku da Real Madrid, inda ya ce wannan wata gagarumar dama ce a gareshi ta sake nuna cewa har yanzu fa ruwa yana maganin dauɗa.