Wani matashi ya yi matukar farinciki bayan budurwarsa ya kai masa ziyara har gidansa yayin da ta yanke shawarar kwana a can, Legit.ng ta ruwaito.
Mutane da dama sun ga yadda matashin ya ba budurwar kyautar sabuwar IPhone don ta maye gurbin waccan tare da fatan ba za su rabu ba.
KLU KARANTA: Bayan kwashe shekaru muna soyayya, saurayina ya auri wata daban, Budurwa ta koka
Matashin mai suna @oluwafemifrancis2, ya wallafa gajeren bidiyon kyakkyawar budurwarsa wacce ya gayyata don ta kwana.
Da safe bayan ta yi bacci ta falka, budurwar ta share gabadaya dakin tare da harabar gidan, ta kuma kwashe gabadaya kayansa masu datti ta wanke.
Budurwar ta kula da saurayin dakyau inda ta dinga ‘yan ayyuka a kicin kafin ta huta. Ya ce ya yi farinciki kan yadda ta yi ayyuka inda ya yi mata kyauta.
Ya fitar da ita waje inda ya sauya mata waya zuwa wata sabuwa Mata da dama sun yi tsokaci karkashin bidiyon inda suka yi fatan saurayin ba zai rabu da ita daga baya ba.
Tirƙashi: Bidiyon Wata Budurwa Mai Aski Da Falleliyar Wuƙa Ya Ɗauki Hankula
Wata budurwa mai yin aski ta karaɗe yanar gizo bayan bidiyon ta ya bayyana inda take yiwa wani aski da wuƙa.
Budurwar mai suna Lydia Williams ta sanya wani bidiyo a TikTok, wanda ya nuna yadda tayi amfani da wuƙar cikin ƙwarewa ta yiwa wani matashin yaro aski.
A cikin bidiyon wanda yanzu haka sama da mutum dubu ɗari da hamsin suka kalle sa, yaron ya zauna yana jiran Lydia ta wasa wuƙarta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Masu bibiyar Lydia a manhajar TikTok sun yaba sosai lokacin da ta sanya wuƙar a kan matashin yaron, ta shige kamar wata reza mai kaifin gaske.