Sa’o’i kaɗan bayan saurayinta ya kirata a waya, wata budurwa mai suna Anita Oghenero John, ta gano cewa ya auri wata budurwar daban.
Budurwar ta sanya hotunan su tare lokacin da suke shan ƙauna, yayin da take ta sharɓar kuka bayan yayi watsi da ita. Jaridar Legit.ng ta rahoto
KU KARANTA KUMA: Ɗanwasan ƙwallon kafa na Najeriya ya kwanta dama ana tsaka da wasa
A cikin bidiyon da ta sanya a manhajar TikTok, Anita ta rubuta cewa:
“Saurayina yayi aure kwanaki kaɗan bayan nayi masa ganin ƙarshe sannna sa’o’i kaɗan bayan mun kammala waya da shi. Ban sani ba ko zan iya warkewa daga wannan ciwon.”
Da take bayyana saurayin nata a matsayin wani iblishi sanye da kayan mutane, Anita ta shawarci mutane da su riƙa jin tsoron kaidin maza inda take tunanin yadda za a iya ta iya warkewa daga wannan ciwon da sanya mata.
Ta kuma sanya bidiyo da hotunan bikin saurayin nata waɗanda aka turo mata ta WhatsApp. Budurwar ta koka cewa suna tare ƴan kwanaki kaɗan kafin auren sa.
Daga Zuwa Neman Aurenta, Budurwa Ta Shararawa Saurayinta Mari a Gaban Jama’a
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta zaɓi da ta kunyata saurayinta a gaban jama’a bayan ya nemi aurenta.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta janyo cece-kuce bayan ta wulaƙanta saurayinta saboda ta nemi aurenta a gaban mutane.
A wani ɗan gajeran bidiyon da majiyar mu tayi kaciɓus da shi a Facebook, an nuna budurwar cikin coci lokacin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta, inda mutane da dama suka taru a wajen.