Wasu miyagun ɗauke da bindigu da ake kyautata zaton ƴan bindiga me sun harbe wani magidanci mai suna Mallam Mannir Abubakar, sannan suka sace matar da ɗiyar sa a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
A cewar rahoton shafin Linda Ikeji, ƴan bindigan sun dira ne a gidan Abubakar wanda yake a bayan otal ɗin Karma sannan suka yi ƙoƙarin sace shi tare da iyalan sa a safiyar ranar Laraba, 29 ga watan Maris 2023.
KU KARANTA KUMA: “Zan saki matata amma sai ta rantse bata taɓa baɗala da wasu mazan ba”, Magidanci ga kotu
Abubakar ya ƙi yarda su tafi da shi, wanda a cewar sa hakan ya sanya ƴan bindigar suka harbe shi sannan suka tafi da matar sa da ɗiyar sa.
Yanzu haka yana wani asibiti a cikin Gusau, inda yake karɓar magani a dalilin raunikan da ya samu daga harbin da ƴan bindigar suka yi masa.
Sai dai ba a san inda iyalan nasa suke ba har ya zuwa yanzu, domin ƴan bindigar ba su kai ga neman su ba.
Babban Hafsan Tsaro ya ba da umarnin ida kakkabe ƴan Boko Haram da ISWAP baki daya
A wani labarin na daban kuma, babban hafsan sojojin ƙasa ya bayar da umurnin a kawo ƙarshen ƴan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
A ranar Alhamis ne babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya ziyarci dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK).
Irabor ya yabawa irin rawar da suke takawa tare da tuhume su da su kawar da sauran masu tada kayar baya da ke ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.