A wani al’amari mai kama da almara, faɗa ta kaure tsakanin yan uwa da iyalai gamida iyalan wani mamaci sakamakon tsokalo tsuliyar dodo da wani ya yi game da rabon gado.
Matsalar ta faru ne yayin da ake tsaka da jana’izar Mamacin inda wani yake tsegumin cewa akwai yiwuwar a yi kwanta-kwanta kan dukiyar da Marigayin ya tafi ya bari.
To jim kadan bayan da wannan magana ta ratsa kunnen ɗaya daga cikin yan uwansa ne dai chachar baki ta kaure, inda har ta kai ga wasu ke nunawa karara irin yadda suke buƙatar a yi rabon arzikin nashi don gudun yin kitso da Ƙwarƙwata.
Ko da yake har yanzu ba a tantance a ina ne lamarin ya faru ba, to amma muryar hayaniya dake cikin faifan Bidiyon damben tana nuni da cewa ya faru ne a kasar Ghana bisa irin harshe da suke amfani da shi.