Wani dan sanda da wasu mutane uku sun rasa rayukansu a ranar Alhamis a Odo Ere hedikwatar karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi a sakamakon rikici da ya barke bayan da aka kama wasu ‘yan fashin da ake zargin ‘yan kungiyar fashi da makami ne da suka mamaye bankuna a ranar Talata.
Mazauna cikin farin ciki sun ce sun yi dandazo ne a ofishin ‘yan sanda da ke Ode Ere da tsakar rana domin murnar samun wannan nasarar.
Sai dai abin takaicin shi ne, mutane uku ne suka mutu a lokacin da wani dan sanda ya zare bindigarsa bisa kuskure don shawo kan gungun jama’a da suka zo domin hango wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi ne da aka kama a ofishin.
Cikin fushin mutuwar ‘yan uwansu, an ce matasan da suka fusata sun hada kansu suka yi wa dan sandan duka har lahira.
Biyu daga cikin wadanda Lamarin ya rutsa da su ‘yan asalin Egbe ne, yayin da mutum na uku ya fito daga wani kauye mai makwabtaka da Igbaru Duro.
Wani dan sanda da ake kyautata zaton an zabo shi ne daga hedkwatar rundunar da ke Abuja domin duba halin da ake ciki a yankin, ya ga yadda lamarin ya faru da misalin karfe 5 na yammacin ranar Alhamis.
Jaridar Daily trust Ta Ruwaito cewa, Duk kokarin tattaunawa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Kogi, abun ya ci tura domin bai dauki waya ba.