Hukumar Kwastam ta Najeriya, shiyar Kano da Jigawa, ta bayyana cewa ta tara kudaden shiga da ya kai N25.3billion a shekarar 2021, kari daga N24.4billion da rundunar ta samu a shekarar 2020.
Rundunar ta ce ayyukan da take yi a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) ya kuma kara habaka kudaden shiga.
Kwanturolan hukumar, Suleiman Pai Umar ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, rundunar ta kuma samu nasarar dakile ayyukan fasa-kwaurin da ta kai ga kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai sama da Naira Milliyan 187 a matsayin Duty Payd Value (DPV) a ayyukan ta na baya-bayan nan.
Kazalika ya ce, Daga Cikin kayayyakin da hukumar ta kwace akwai, buhunan shinkafa 1040 na kasar waje da kudin su ya Kai naira miliyan 69, spaghetti na kasashen waje da darajarsu ta kai Naira miliyan 63.9, da kuma fatar jaki 339 da ta haura Naira miliyan 31.
Ya ce a duk shekarar 2021, rundunar ta kama jimillar mutane 398 tare da haramtattun Kayayyaki na sama da Naira biliyan 1.