Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin bude gidajen Kallo a fadin jihar tare da musu kashedin bin dokar da masana suka gindaya domin dakile cutar sarke numfashi ta Corona.
Hakan ya biyo bayan fara gasar kwallon kafar Laliga ta sakar Andulus da aka yi a jiya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ga shugwabannin gidajen kallo da suka kai masa ziyara a ofishinsa, a jiya Juma’a.
Domin ganin gidajen kallon sun bi dokar da aka shimfida, gwamna Ganduje ya basu gudunmawar takunkumin hanci har guda dubu Arba’in (40,000).
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-kulle-najeriya-ta-sake-kwaso-mutane-102-daga-kasar-masar/
“Mun yanke wannan hukunci ne domin mu bawa masu sanan’o’i damar yin kasuwancinsu, saboda mu kara fadada tattalin arzikinmu”. Cewar Ganduje.
Gwamnan ya yi kara kira ga masu gidajen kallon da su yi amfani da wannan damar wajen fadar da jama’a illar cutar da kuma hanyoyin magance ta.
Shugaban kungiyar masu gidajen kallo na jihar Kano, Sharu Rabiu Ahlan ya jinjinawa gwamna Ganduje kan wannan irin namijin kokari da yayi na basu damar ci gaba da gudanar da al’amuransu na yah da kullum.
“Muna matukar godiya da takunkumin da gwamna ya sa a ka bamu, kuma ina mai tabbatar masa da cewa zamu bi dokokin da aka shimfida masa, zamu kasance masu biyayya”. Cewar Ahlan.