Ana sa ran Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango za ta tattauna da tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar, kan janye dakarun wanzar da zaman lafiya da zai dace da bukatun jama’a. Kamar yadda mai magana da yawun gwamnati kasar Patrick Muyaya ya sanar.
Sanarwar na zuwa ne bayan da shugaba Félix Tshisekedi ya jagoranci wata ganawa da shugabannin majalisun dokokin biyu, da firaminista da kuma jami’an lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin kasar.
Mummunar zanga-zangar neman korar Jami’an wanzar da zaman lafiya na majalissar dinkin duniya wato, Monusco ta barke a arewacin Kivu, da Garin Goma, a ranar 25 ga Yulin shekarar 2022, kuma tun daga lokacin ta fara bazuwa zuwa wasu sassan kasar ta Jamhoriyar Dimokuradiyyar Congo.
Masu fafutuka na zargin tawagar Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen dakatar da tawayen da aka kwashe shekaru ana yi a gabashin kasar.
KARANTA WANNAN LAABRIN: Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB—Baba Ahmed
Da yake jawabi a ranar Litinin Mista Muyaya yace an kashe mutane 36 da suka hada da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya hudu yayin zanga-zangar.
Ya kara da cewa, “Saboda abubuwan da suka gabata, an umurci gwamnati da ta gaggauta ganawa da wakilan jami’an Monusco don sake nazarin shirin janyewarta da aka cimma a karkashin kudurin kwamitin sulhu mai lamba 2556.
Wannan na zuwa ne yayin da Jami’an tsaro suka tarwatsa wata sabuwar zanga-zanga a Beni da ke arewacin Kivu, a ranar Litinin wanda ta kawo cikas ga al’amura yau da kullun a yankin.
A halin da ake ciki kuma, mutane da dama sun jikkata yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a lardin Tsopo da ke arewacin kasar.
Kazalika rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta shafe fiye da shekaru 20 tana aiki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin da jami’an na Monusco suka karbi ragamar jagorancin aikin tun a shekarar 2010.