Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, ba ya goyon bayan kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra wato (IPOB) da ayyukanta.
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV a ranar Litinin.
“Ban yarda da cewa Peter Obi yana goyon bayan IPOB ba saboda ba zan kasance tare da shi ba a yau (idan yana goyon bayan su),” in ji shi.
Ya lura cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe balantana makama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Jam’iyar PDP Sama Da 2,500 Sun Koma APC A Jihar Kebbi
Ya ce, “irin hirar da suka yi da ni lokacin da na ce ina so a yi min magana a zaben 2023 a matsayina na dan Najeriya. Babu wani abu da mutane ba za su iya cewa ba. A safiyar yau, dole ne in yi taron manema labarai don yawan labaran karya a duk faɗin duniya … waɗannan zarge-zargen har yanzu ba su da tabbas.”
Baba-Ahmed ya kara da cewa kafin ya amince ya zama abokin takarar Obi, ya yi duk binciken da zai iya kuma babu abin da ya danganta tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyar IPOB.
Ya ce, “Misali, sun ce an yi wa ’yan Arewa rashin adalci ta hanyar sanya katin shaida, kafin na yanke shawarar shiga tafiyar Peter Obi. A cikin makonni na yi duk binciken da zan iya. Tuni dai wayoyin hannu na dauke da kyamarori, na nemi har ma na bayar da diyya ‘ko zan iya ganin hoton wanda ya tsaya ya ce lokacin da Peter Obi yake gwamna a jihar Anambra, ga wani abu da yayi na goyon bayan IPOB, Wannan ya sanya ni na saka wannan?’ .
“Kuma bai kamata in zauna in yi imani da mutanen da ba su da hankali ba, saboda suna magana ko ta yaya kawai saboda kun fito siyasa lokacin da kowa ya san irin siyasar da akeyi a kasar nan.”