Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta sha alwashin zurfafa bincike kan jami’an ta da suka ci zarafin wani dan jarida mai aiki da kamfanin Jaridar Vanguard.
A kwanakin baya ne dai jami’an na DSS aka ruwaito cewa sun kuntatawa Gbemiga Olamikan mai daukar hoto a Vanguard.
Da yake tsokaci game da faifan bidiyon da ya yi ta yawi a kafar sadarwar WhatsApp a ranar Talata Kakakin Rundunar Dakta Peter Afunanya ya ce Ayyukan rundunar ba zai yi sako-sako da tafiya tare da yan jarida ba jana ba zai zura idanu ya ga ana cin zarafin au ba.
Ya ce “DSS runduna ce ta kowa kuma abokiyar hulɗar yan jarida ne, ba za mu zu
ra ido mu ga ana cin zarafin su ba”
Ya ce akwai dangantaka mai kwarin gaske tsakanin bangarorin biyu, don haka babu hujjar da za ta sa kuma ta bari wani abu mara kyawu ya gibta tsakani.