Jami’an rundunar tsaro ta Civil Defense a Jihar Kebbi sun yi nasarar chafke mutane biyu da aka yi hayarsu su lashe wani mutum.
Mutane dai an yi kwangilar su da aniyar hallaka wani mutum mai suna Gari Mamman mazaunin kauyen Lahore dake karamar hukumar Zuru ta Jihar ta Kebbi.
Kwamandan rundunar ta Civil Defense Alhaji Suleiman Ibrahim Marafa ya ce bisa bayanai da suka samu a gurin wadanda ake zargin, wani mutum ne mai suna Alhaji Mamman ya yi hayarsu da zummar wancan aika-aika, inda ya basu fashin alkalami naira dubu sittin cikin dubu tamanin da aka yi yarjejeniya.
Ya ce mutanen biyu masu suna Mando da Manu, sun banka wa gidan Gari Mamman amma daga bisani sun fahimci cewa ba ya gida.
Sai dai a wata tattaunawa da manema labarai, wanda ya bada kwangilar kisar ya musanta zargin, inda ya ce shi dai tura su ya yi su koya mishi hankali ba wai kashe shi ba.
Ya ce kuma dalilin shi na haka shine, yana zarginsa ne da hallaka mishi mahaifi watanni uku da suka wuce.