Sufeton ‘yan sanda na ƙasa Muhammad Adamu ya ce ƙa’idojin da rundunar ta shimfiɗa wajen shiga aiki suna nan daram, kuma shakka babu sai kowa ya bi su kafin shiga tsarin aikin na ɗan sanda.
Muhammad Adamu ya ce ya zama wajibi duk mai shirin shiga aikin ɗan sanda ya cika ƙa’idojin da aka zayyana a sashe na 71 zuwa 75 na kundin dokokin hukumar ‘yan sanda.
Ya ƙara da cewa, duk matashin da yayi nasara a yayin cike fam din shiga aikin ɗan sanda a yanar gizo, to za’a gayyace shi don tantancewa da aka fara tun daga jiya 24 ga watan da muke ciki na Agusta, zuwa 6 ga watan Satumba a cibiyoyi daban-daban dake faɗin ƙasar nan.
Har wa yau, Sufeton ‘yan sanda ya kuma hori jami’an dake tantancewar da su maida hankali, wajen baiwa duk wanda ya cika ƙa’ida damar da kundin dokokin hukumar ‘yan sanda ta tsara su bashi.