Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i ya sallami wasu masu mukaman siyasa 19 a Jihar.
Wannan na fitowa e ta bakin Babban mai baiwa gwanan shawara kan yada labarai sa Sadarwa Muyiwa Adekeye a yau laraba inda aka watsa shi wa manema labarai.
Wadanda aka sallamar sun hada da Bala Muhammad Mataimakin Shugaban ma’aikata na Majalisa, Halima Nagogo Babbar Hadimar Gwamnanda Umar Abubakar mataimakin hadimin gwamna da Ben SD Kure Babban Mai tallafa wa gwamna kan harkokin siyasa hadi da Mustapha Nyusha da Jamilu Dan-mutum.
Sauran sun hada da Babban Hadimi kan harkokin siyasa da Zainab Shehu Mai bada shawara kan harkokin bunkasa al’umma da stephen Hezron sai Muhammad Shuaibu da Aliyi Haruna hadi da Halima Idris.
Sai kuma Aliyu Salihu, Ashiru Zuntu Saida Sa’ad da Elias Yahaya da Tasiu SULEIMAN Yakaji sai Samuel Hadwayah da kuma Ahmed Muhammad Gero.
A watan Afirelu gwamna el-Rufa’i ya bayyana aniyarsa ta sallamar wasu maaikata bisa dalili na karancin kudi.