Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya sha alwashin janye dakarun sojin Faranss daga kasar Mali muddin rikicin siyasar kasar ta ya yi shirin rikida zuwa wani abu na addini.
Wannan mataki na Macron ya zo ne daidai lokacin da kasar ta fuskaci juyin mulki karo na biyu cikin watanni tara kachal.
Shugaba Macron ya yi gargadin cewa Mali na ƙoƙarin rikidewa zuwa ƙasar Muslunci, don haka sai an tashi tsaye don kawar da hakan.
A yanzu haka Faransa na da dakarun soji sama da 5,000 a yankin sahel wadanda su ne ke jagorantar yaki da tsattsauran ra’ayi.
Tun a shekarar 2013 Faransa ta jibge dakarunta a kasar Mali da Mauritania da Nijar da Burkina Faso da kuma Chadi don yakar tsattsauran ra’ayin.