Jami’an rundunar yaki da ingiza mai kantu ruwa a Jihar Imo sun bindige wasu ƴaƴan Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB sa suka yi yunkurin bankawa Ofishin Yan Sanda wuta.
Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan da wasu ƴaƴan Ƙungiyar suka lalata ofishin rundunar da kuma wata kotun Majestire a Kauyen Atta sake Jihar.
To sai dai cikin nasarar Ubangiji wadannan yan bindiga sun gamu da ajalinsu ba kamar na kauyen Atta da suka ci banza ba, yayin da wasu daga cikin su suka tsere da raunukan alburushi a jikinsu.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Bala Elkana wanda shi ya tabbatar da sahihancin wannan labari, ya ce al’amarin ya auku a almurun jiya asabar inda aka shafe sa’o’i uku zuwa hudu ana ɓarin wuta tsakanin bangaren yan sandar da na yan IPOB din.