Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta daidaita tarihin lashe babbar gasar Premier a ranar Asabar, bayan da ta lallasa Bournemouth da ci 9 da nema.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa was an an buga shi ne a filin wasa na Anfield, kuma wannan wasa ya shiga cikin tarihi musamman irin namijin kokarin da suka yi.
KARANTA ANAN: Yajin Aiki: ASUU Ta Musanta Batun Cewa Jami’o’in Jihohi Basu Da Amfani
Roberto Firmino da Luis Diaz ne suka zura kwallaye biyu a ragar, yayin da Harvey Elliott da Trent Alexander-Arnold da Virgil van Dijk da Fabio Carvalho da Chris Mepham suma suka kara tasu kwallayen.
Nasarar Liverpool ta yi daidai da wadda Manchester United ta doke Ipswich a 1995, United ta doke Southampton da ci daya a bara, yayin da Leicester kuma ta ci Southampton 9-0 a 2019.
A wani labarin kuma: Rikicin PDP: Ayu Zai Sauka, Tsagin Wike Za Su Fitar Da Shugaban Jam’iyya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na fuskantar matsananciyar matsin lamba daga magoya bayansa biyo bayan rahotannin da ke cewa ya ki amincewa da bukatar gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike na tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu.
An tattaro a Abuja, a ranar Juma’ar nan cewa, an cimma yarjejeniyoyin da dama bayan ganawar ido da ido tsakanin Atiku da Wike a Landan. Wani bangare na yarjejeniyar dai an gano shi ne cewa a baiwa Ayu damar sauka mai martaba tare da ba shi masauki a sabuwar gwamnatin PDP idan an kafa ta.