Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta karyata rahoton da ya ke cewa ta bayyana sunan da ta ayyana jami’o’in mallakin gwamnatocin Jihohi.
DAILY POST ta rawaito cewa a ranar Juma’ar nan ne kafafen yada labarai da dama suka cika da martani dangane da ikirarin da Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi na cewa jami’o’in Jihohi na cikin rudani don haka bai kamata a dauke su da muhimmanci ba.
Ku tuna cewa Farfesa Osodeke a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana a gidan talabijin na Arise TV inda ya yi magana kan wasu batutuwa dangane da ci gaba da yajin aikin jami’oi da ASUU ta fara tun watanni shida da suka gabata.
Da yake magana game da wasu jami’o’in Jihohi da suka fice kwanan nan daga fafutikar, shugaban ASUU ya ce, “Ku yi magana a kan muhimman jami’o’i ba irin wadannan ba. Ba sa cikin yajin aikinmu”.
Karanta kuma: Jami’o’in Jihohi A Najeriya Basu Da Amfani – ASUU
Wannan ci gaban dai ya jawo cece-ku-ce daga wasu jami’o’in jihar da kuma ‘yan Najeriya da suka damu da shugaban kungiyar ASUU bisa zargin sanya wa jami’o’in jihar suna ‘marasa amfani’.
Ku tuna cewa Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Osun (UNIOSUN), Farfesa Odunayo Clement Adebooye yayin da yake mayar da martani kan rahoton jiya, ya bayyana shugaban ASUU a matsayin mai rikon sakainar kashi.
Farfesa Adebooye ya ce Jami’ar Jihar na da ma’aikata masu cikakken lokaci guda 481 kuma a cikin su, 387 suna da cikakken Ph.D. “Wannan ba gaskiya bane.”
Sai dai da yake magana da DAILY POST a ranar Asabar, shugaban ASUU ya karyata rahoton yana mai cewa kafafen yada labarai sun yi masa kuskure.
A cewar Osodeke, yana magana ne kan jami’o’i uku kacal mallakar gwamnatocin Jihohin da a halin yanzu ba sa yajin aiki.
Da yake bayyana rahoton a matsayin na bogi, Osodeke ya koka da rashin sanin makamar aiki a cikin rahoton, inda ya yi zargin cewa kafafen yada labarai na da nufin haifar da rudani a cikin tsarin.
Ya ce, “Babu wani abu makamancin haka. Karya ce. Na gaya wa kaina cewa ba zan sake yin magana da manema labarai ba domin koyaushe suna kuskuren gabatar da abubuwa.
“Na gano cewa jaridun Najeriya sun kware wajen sarrafa tambayoyi, suna ba da rahoton abin da wani bai fada ba don kawai haifar da rudani a cikin tsarin. Ba za su ba da rahoton abubuwa yadda yake ba.”
A wani labarin kuma: KASU ta yi Allah wadai da kalaman Shugaban ASUU akan Jami’o’in Jihohi
Hukumar gudanarwar Jami’ar Jihar Kaduna, a ranar Asabar ɗin nan, ta caccaki Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa, ASUU, Farfesa Victor Emmanuel Osodeke, kan kalaman da ya yi na cewa wasu jami’o’in mallakar Jihohi a Najeriya basu cancanta ba, kuma basa bada ingantaccen ilmi.
Shugaban ASUU, a lokacin da yake tattaunawa kai tsaye kan wasu al’amura na Ƙungiyar, ya bayyana wasu jami’o’in mallakar Jihohi a Najeriya a matsayin bara-gurbi.