Rahotanni masu zafi sun bayyana cewa Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi auren sirri da budurwarsa mai suna Carrie Symonds a wani Katafaren coci dake birnin Westminster na kasar.
An gudanar da daurin auren ne a gaban yan uwa da abokan arziki kawai ba tare sa hallartar wani bare ba, kamar yadda jaridun Birtaniya da dama suka ruwaito.
Toh sai dai har yanzu babu wata magana a hukumance dangane da wannan al’amari, yayin da su ma jama’ar gari suka ja bakin su suka yi gum.
Ya siyasa a kasar sun yi ta mika sakonsu na fatan alkhairi wa Mista Johnson, kasancewarsa Firaminista na farko dake karagar mulki da ya yi aure tun bayan shekaru 200 da suka shuɗe.
Jaridar Mail ta labarto cewa mutane 30 kachal aka gayyato a izuwa bikin, bisa la’akari da cewa iya adadin mutane kenan da za su taru, kamar yadda dokar Korona a kasar ta sahale.
Su ma mutanen da aka gayyata ɗin an faɗa musu ne a kurarren lokaci, yayin da kuma aka umarci mambobin Cocin birnin Westminster da su bar gurin kafin karfe daya na rana.
Da ma dai a ranar 29 ga watan Afirelun shekarar da ta gabata ne budurwar Mista Johnson din ta haihu, bayan shafe shekaru suna kwashe soyayya.