Wasu Fursunoni yan Najeriya da ke gidan yarin Kaliti, wanda shi ne gidan yari mafi girman tsaro a birnin Addis Abba na kasar Habasha, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sassauta ta dawo da su gidajen yari a Najeriya.
Fursunonin na neman a ba su damar ci gaba da zaman gidan yari a Najeriya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Fursunonin sun ce suna fuskantar cin zarafi na danne hakkin bil adama a gidan yarin.
Akwai ‘yan Najeriya sama da 200 a gidan yarin Habasha, wadanda har yanzu wasunsu na jiran shari’a.
KU KARANTA KUMA An Fara Tattaunawa Don Kwamce Damarar Yaki Tsakanin Habasha Da Yan Tawaye
A wata wasika da fursunonin suka aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ofishin jakadancin Najeriya a kasar Habasha, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki.
Sun koka da yunwa, rashin samun kulawar likita, jinkirin hukunci da kisa da kuma cunkoso.
“ Fursunonin Najeriya da ke Kaliti a gidan yari na Habasha suna neman taimako daga gwamnatin Najeriya; muna rokon gwamnati ta kawo mana agaji cikin gaggawa.
“Ba mu da damar samun ruwa, abinci da kuma kula da lafiya.
“Muna rokon gwamnati ta sa baki domin mu ci gaba da zaman gidan yari a Najeriya. Yawancinmu sun kamu da rashin lafiya saboda rashin abinci mai gina jiki, kayan aikin kiwon lafiya sun yi karanci, kuma fursunonin na fama da matsalolin lafiya,” a sassan wasikar.
Fursunonin sun ce saduwa da iyalai da abokai a wajen Habasha ba zai yiwu ba.
Sun nuna nadama game da abin da suka aikata tare da neman “zama na biyu don gyarawa”.
Wannan dai ba shi ne karon farko da suka nemi a mayar da su gidan yarin Najeriya ba. A shekarar 2021, fursunonin sun yi tir da halin da suke ciki na rashin rayuwa mai kyau, suna rokon Gwamnatin Tarayya ta kawo musu dauki.
Haka kuma a shekarar 2019, wani Chika Nwachukwu ya yi tsokaci game da mummunan halin da ‘yan Najeriyar da ke tsare a cikin ginin. Sai dai kokarin da suka yi bai haifar da sakamakon da ake so ba.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Akwai rahotanni da dama da ke bayyana halin da ‘yan Najeriya ke ciki a gidan yarin na Kaliti. An bayar da rahoton cewa fursunonin suna jure yanayin da ya yi hannun riga da ka’idojin kare hakkin bil’adama.
A watan Agustan 2019, an bayar da rahoton cewa wani dan Najeriya Odemu Efe ya mutu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a wurin.
A Wani Labarin Kuma Bamu Samun Isassun Sabbin Kudade Daga CBN Ba – Bankunan Kasuwanci
Ma’aikatan bankunan kasuwanci a kasar nan sun tunkari babban bankin Kasa (CBN) kan ikirarin cewa bankunan na da isassun kudade na naira a cikin rubunsu amma suna tarawa.
Bankunan sun yi tir da babban bankin na CBN ne a lokacin da jami’ansu suka bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken karancin sabbin takardun kudi da kuma wa’adin da babban bankin ya bayar a ranar 31 ga watan Janairu.