Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da kawo shirin ke fasalin naira saboda ya kasa samun takarar shugaban ƙasa.
Godwin Emefiele an yi ta alaƙanta shi da neman takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya musanta bayan wasu sun siya masa fam ɗin takarar na naira miliyan ɗari.
KU KARANTA KUMA: Ƴan sanda sun ceto ragowar ɗaliban firamare da aka yi garkuwa da su
Jaridar Daily Trust ta ambato gwamna Ganduje bayan sun gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, yayi zargin cewa Emefiele baya son yaga anyi zaɓen dake tafe.
Ganduje ya bayyana cewa sun gayawa shugaba Buhari cewa sauya fasalin naira zai janyo baƙar wahala ga ƴan Najeriya.
“Wannan ba shirin APC bane, shiri ne na waɗanda suke kewaye da shugaban ƙasa da gwamnan babban bankin Najeriya. Kun san cewa Emefiele ya so ya zama shugaban ƙasa amma bai yi nasara ba. Wannan dalilin ya sanya baya son ayi zaɓe ko ya gwammace ace wata jam’iyyar tayi nasara.” A cewar sa
Da aka tambaye shi ko gwamnonin za su raba gari da shugaban ƙasa kan wanann shirin, sai ya kada baki yace:
“Aa muna adawa ne da wannan shirin na sauya fasalin naira na gwamnan babban bankin Najeriya da kuma waɗanda ke kewaye da shugaban ƙasa.”
An kuma: Wani Mutum Ya Faɗi Matacce a Layin Cirar Kuɗi a Banki
A wani labarin na daban kuma, wani mutum ya yanke jiki ya faɗi yana kan layin cirar kuɗi a banki.
Wani abun ban takaici ya sake aukuwa inda wani mutum ya faɗi ya mutu a cikin banki a yayin da yake ƙoƙarin ciro kuɗi.
Lamarin ya auku ne wani bankin kasuwanci dake a Agbor, jihar Delta, a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Mutumin wanda ba a san kowane ne ba, ya faɗi ya mutu ne bayan ya kwashe dogon lokaci akan layin cirar kuɗi a bankin.