Wata ƴar Najeriya mai amfani da sunan @talk2veee a Twitter, ta caccaki wuraren siyar da abinci masu yin ɗan gwashe, onda ta yi mamakin cewa ko hakan yana ƙara mu su yawan ribar da suke samu ne.
@talk2veee ta yi tsokacin ne a Twitter lokacin da ta banƙaɗo wani abu da ta gano lokacin da ta je kai markaɗen tumatur da tattasai, Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Zaben 2023: Cikakken Jerin Alkalai 257 Da Za Su Saurara Korafe-korafe
Ta bayyana cewa lokacin da ta ke a wajen injin markaɗen, wata mata ta zo ɗauke da kwanon ta cike da wasu abubuwa da a ganin ta kwandon shara ya dace da su. Tace matar ta bayar da umurnin a wanke su sannan a niƙa mata su.
@talk2veee ta zargi wasu masu abincin bakin titi da yin amfani da bagen tumatur, tattasai da albasa wajen yin abincin su, inda ta sanya hotunan kayayyakin da matar ta kawo a markaɗa mata.
@talk2veee tace matar na barin wajen, mai yin markaɗen ta yi ta maganar yadda mutane masu zuwa gidan cin abinci suke cin kwashe-kwashe.
A kalamanta:
“Na siyo tumatur da tattasai masu yawa, na tsaya a markaɗa min su sai na yi kaciɓus da wani abu…
“Ba zan iya zargar duk masu wajen cin abinci haka suke yi ba, amma wasu daga cikin su suna siyan bagen tumatur, tarugu da albasa gwanin arha. Daga nan sai su markaɗa su haɗa da tumatur na gwangwani.”
The other lady that was told to wash them, kept hissing and complaining in her native language
The remaining ones in the black bowl, was what she could salvage cos they were literally rotten
Why joke with what people eat?
Does it increase their profit margin? pic.twitter.com/3rPgybGBz8— Talk2veee (@talk2veee) April 24, 2023
Yadda Wasu Manoma Suka Yi Amfani Da Asiri Domin Korar Wanda Ya Ba Su Aron Inda Suke Noma
A wani lokaci can baya, wani ɗan Najeriya ya siya fili mai girma eka 10 sannan ya bayar da jinginar ta ga wasu manoma.
Dalilin sa na yin hakan shine yana da sauran abubuwan da ya ke yi kuma bai shirya ya fara aiki a cikin gonar ba.
Comments 1