Tsohon dan wasan Super Eagles, Julius Aghahowa, ya ce Gernot Rohr ba zai iya daga Darajar Super Eagles a matsayin koci ba.
Da yake magana a shirin SuperSport, Naija Made, Aghahowa ya ce Rohr ya kasa taka rawar gani a Najeriya.
“Idan ka yi maganar ’yan wasa masu hazaka suna nan, ’yan wasan suna da kwarewa amma ba mu da kocin da zai iya fitar da gwani a cikin wadannan ’yan wasan. Na ga wasu ‘yan wasa biyu da bai kamata su kasance a tawagar da ta bugawa da Nigeria wasa a ranar ba,” in ji Aghahowa.
Ya kuma yi magana game da rashin gwanintar Eagle a tsakiyan fili.
“Ba mu da mai yin wasa da Kwallo a tsakiyar fili. Ina tsammanin wani yana sanye da lambar ɗan irin wadannan Yan wasan, “10”, amma da kuka ga Dan wasan ba zai iya ɗaukar ƙwallon ba, ya Dan abokan hamayya, kafin ya saki fasin ga abokin wasan shi.
“Kuna ba da fasin lokacin da babu wanda ya yi muku alamar zai iya rikewa, don haka ta yaya za mu ci gaba daga wannan salon wasan kwallon kafa da muke takawa. Ba na jin za mu iya ci gaba kamar haka? ”
Rohr dai ya fuskanci matsin lamba inda rahotanni ke cewa hukumar NFF na tunanin korar shi kafin gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a watan Janairun shekara Mai zuwa 2022.