Tsohon dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya ce lallai Ƙungiyar Tottenham ba ta yi farar dabara ba wajen korar Kocin ta Jose Mourinho kwana kadan gabannin wasan karshe na kofin kalubalen kasar Ingila.
Rooney ya ce bai kamata a ce Spurs ta dauki wannan mataki ba, kamata ya yi a cebta bar dan kasar Portugal din mai shekara 58 har sai bayan wasan karshen gabannin daukar matakin korar tashi.
Tottenham ta gamu da wata mummunar Mashashshara a wannan kaka lamarin da ya kai ga magoya baya suka yi ta nuna rashin gamsuwar su kan taohon kocin FC Porto da Chelsea da Inter Milan da Real Madrid wanda ya maye gurbin Mauricio Pochetino a Ƙarshen Shekarar 2019.
“A gani na gurguwar dabara ce daukar wannan mataki dabda wasan karshe na Carabao, gaskiya wannan bakon al’amari ne. Zahirin gaskiya ya kamata su dan jinkirta mishi har an yi wasan karshe na kofin Kalubalen indai lallai hakan suke so”
“Mourinho Koci ne fatan ganin ko da yaushe ya lashe kofuna, kuma ya lashe kofuna da dama a harkokin shi na horaswa. Gaskiya Shugaban Tottenham Daniel Levy ya yi ragon azanci na korar a daidai wannan lokaci.
Kuma tuni dan wasan Tottenham Son Heung-min ya taya Mourinho fatan alkhairi a nan gaba