Shugaban Hukumar Kula da ingancin Kayayyaki ta Kasa SON Mallam Farooq Salim ya yunkura don samun goyon bayan gwamnatin tarayya da ta bar hukumar rika binciken ingancin Kayayyyaki daga bakin ruwa gabannin shigo da su kasa.
Mallam Farooq ya mika wannan bukata ce yayin da yake wata ziyarar gani da ido a Katafaren Kamfanin Sarrafa Tama da karafa ta KAM Holding dake birnin Ilori.
Ya ce “Ina so a sani, rashin bada hukumar SON damar gudanar da cikakken bincike kan ingancin Kayayyaki a bakin ruwa, yana taka rawa matuka wajen shigo kayayyaki marasa inganci.”
“A Kasar ku Najeriya ne kawai za ka an takaita aikin hukumar ita ce kaɗai aka san tana da alhakin kula da ingancin Kayayyaki musamman zuwa bakin ruwa, kuma haka babban kalubale ne ga tattalin arzikin kasa” Cewar Salim.
A bangaren shi Shugaban Kamfanin KAM Holding na Jihar Kwara Alhaji Kamoru Yusuf ya ce akwai bukatar sake farfado da shirin binciken kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa musamman ma na makamai.
Daga bisani ya jaddada wa hukumar SON cewa Kamfanin zai yi duk mai yiwuwa na ganin ya karfafa bangaren fasahar zamani don ganin an ci gaba da samun ingantattun tama a kasar nan.