Hausawa dai suka ce kowa ya san na faɗa bai san na mayarwa ba.
A kwanakin nan ne dai wani matashi sanye da rigar sarki ya saki wani bidiyo dake kushe dsliban da suka Rubuta jarabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, inda cikin Bidiyon ya kira su da dakikai.
Da ma dai a karshen mako ne hukumar JAMB ɗin ta saki sakamakon jarabawar, sakamakon mafi muni a tarihin JAMB.
To sai dai bayan bayyanar wannan faifan bidiyo ne na matashin mai sanye da rigar sarki, matasa a fadin kasar nan suka yi mishi caaa.
Wata kila kuma lamarin ne ya kai ga matashin ya sake fitowa da wani sabon bidiyo na neman yafiya ga ɗaliban JAMB ɗin, inda ya ce lamarin ne ya fusata shi.