Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa ya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari Mai gaskiya ne da rukon amana, “Kuma Yana bacci ne tare da Naijeriya a zuciyar shi”.
Ya ce Shugaban Buhari ya yi Matukar kokari wurin yin Samar da ababen more rayuwar al’uma, da cigaban su, da kuma daukan matakan da suka dace, wajan farfado da tattalin arzikin kasar nan.
Gwamnan ya kuma yaba wa shugaba Buhari, kan shirye-shirye sa na bunkasa tattalin arzikin kasar nan, musammanma tsarin bai wa Manoma bashi, da kuma bai wa Masu kananan sanao’i jari. NSIP
Badaru ya bayyana hakan ne a wurin taron tarban Tsohon Sanatan Adamawa ta Kudu, Grace Bent, Wanda ya sauya sheka daga jami’iyar adawa ta PDP, zuwa Jam’iyar APC Mai Mulki a ranar Asabar, a garin Yola babban birnin jihar ta Adamawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru da wasu Mutum 13
Gwamnan na jihar Jigawa ya kara da cewa, “Gwamnatin Buhari ta yi matukar kokari, wurin bunkasa hanyoyin kasar nan, Layin dogo, harkan sufurin jiragen Sama, da kuma tabbatar da samun ingantacce wutar lantarki, gami da fitar da tsare-tsaren bunkasa rayuwar al’uma, da yunkurin magance matsalar tsaro daya addabi kasar nan” a cewar shi.
Kazalika ya ce, ” Buhari Mai gaskiya ne da rukon amana, kuma ya na kwana da Naijeriya a zuciyar shi” inji shi.
” Al’umar Naijeriya sun fara ganin tagomashin Mulkin Shugaba Buhari ta kowani bangaren, inda kuma sukafara tururuwan dawowa jam’iyar APC” inji Gwamna Badaru.