By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya tallafawa marayu 200 daga sassa daban daban na kananan hukumomi 17 na jihar da kudi naira 50,000 kowannen su.
Buni ya ce an yi hakan ne don a taimaka musu da dan jarin fara sana’a bayan samun kwarewa.
DUBA WANNAN LABARIN: Kungiyar Kare Hakkin Bil-Adama Ta Yi Allah-Wadai Da Nadin Magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Kwara
“Fatan mu ne cewa wannan taimakon zai karawa rayuwarku zuwa gaba wajen rike kawunan ku,” in ji gwamnan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shekarun marayun sun kasance daga shekara 9 zuwa 14.
Ustaz Babagana Malam Kyari, babban jami’in shirin kuma mai ba Gwamna Buni shawara kan harkokin addini, ya ce wannan shi ne karon farko da aka tallafa wa marayu da yawa a fadin jihar.
Ya ce hakan zai rage ya waitar karuwar barace-barace a kan tituna, musamman marayun da ba su da sana’ar yi.
Kyari ya yi kira ga masu kula da marayun da su tallafa musu tare da tabbatar da yin amfani da kayan a bisa gaskiya da rikon amana.
Comments 1