By Abbas Yakubu Yaura
Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Rt. Hon. Abubakar Sulaiman, a daren ranar Asabar ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP mai mulki.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamna Buni Na Jihar Yobe Ya Tallafawa Marayu 200 Da Kudi Naira 50,000 Kowannensu
Abubakar, wanda shi ne shugaban taron shugabannin majalisun dokokin jiha, ya bayyana haka a lokacin buda baki na watan Ramadan da gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya shirya wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP daga kananan hukumomin Ningi, Toro, Warji da Dass, a Gidan Gwamnati jihar Bauchi.
Shugaban majalisar ya ce ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne saboda la’akari da kyakkyawan salon jagoranci na Gwamna Mohammed da kuma jajircewarsa na kawo sauyi a jihar.
A cewarsa, ci gaban Gwamna Mohammed ya sa shi (kakakin majalisar) ya koma jam’iyya mai mulki a jihar.
Daga nan Sulaiman ya yabawa gwamnan kan abin da ya kira iyawarsa (Gwamna Mohammed) na tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa na gwamnati da majalisar dokokin jihar.
A cewar shugaban majalisar, gwamnan ya samu nasarar hakan ne duk da rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, inda ya ce dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu ta ba da damar tsarawa da aiwatar da tsare-tsare da masu ra’ayin jama’a a jihar.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Gwamna Mohammed ya bayyana cewa babban abin alfahari ne bisa abinda shugaban majalisar ya yi masa.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta zabi fara gudanar da ayyukan raya kasa a fadin jihar da nufin samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar maimakon bunkasa cin hanci da rashawa ta hanyar raba dukiyar gwamnati a tsakanin wasu tsirarun mutane.
Daga nan sai ya nemi goyon baya da hadin kai da gwamnatinsa, da nufin tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a jihar Bauchi.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hamza Koshe Akuyam, ya yi maraba da shugaban majalisar zuwa PDP, inda ya bayyana cewa Sulaiman na daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa da suka koma jam’iyyar ta PDP.
A cewarsa, tare da aiki da iyawar jam’iyyar PDP, za ta samu nasara a zaben 2023 a jihar da ma kasa baki daya.
Comments 1