Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da ya sanya a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Lalong ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi ga al’umar jihar a safiyar yau Litinin.
A cewar shi, ” Sabuwar dokar ta hana zirga-zirga za ta fara aiki ne daga 6 na yamma, zuwa karfe 6 na safen kowace rana, Wanda zata fara aiki a yau Litinin 30 ga watan Agustan nan da muke ciki.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutum 2 a wani gari dake jihar Rivers
“Karamar hukumar Bassa da Jos ta Kudu a yanzu dokar su ta koma daga karfe 10 na dare, zuwa karfe 6 na safe, har’izuwa fitar da wata sanarwa.” a cewar shi.
Kazalika ya kuma ja kunnen masu tada tarzoma da su guji jefa rayukan mutane a cikin hadari, ko Kuma su fuskanci fishin Gwamnati, inda ya ce, tuni a ka bai wa hukumomin tsaro umarnin su magance duk wanda ke kokarin tayar da zaune tsaye a jihar.
A karshe Gwamna Lalong ya ce, bayan duba dokar karamar hukumar Jos ta Arewa , Hukumomin tsaro za su kafa shinge na din-din-din a inda mutane ke taruwa, tare da jami’an tsaro sanye da Kanki, da kuma wadanda za su sa fararan kaya, domin lura da yadda mazauna garin ke ciki.