Wasu Yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, a safiyar yau Lahadi, sun farmaki garin Ka-Bori dake karamar hukumar Khana na jihar Rivers.
Wani shaida dake yankin ya bayyana cewa, yan bindigan sun kashe wata mata da wani magindanci.
Ya kara da cewa, yan bindigan sun kuma raunata wata mata da harbin bindiga, wanda yanzu haka, an kai ta asibiti domin duba lafiyar ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a garin Jos
Sai dai ya zargi wasu mutane dake yankin Kono, na garin Bonue da kai harin
Kazalika ya ce, jami’an yan sanda da wasu hukumomin tsaro sun isa yankin da lamarin ya faru, domin tabbatar da komai ya dai-daita.
Wani mazaunin garin Bori Wanda ya bukaci a sakaye sunan shi, Sabida lamari na tsaro, ya shaida wa majiyar jaridar Dimokuradiyya cewa, sun Jiyo karar harbe-harbe a yankin Ka-Bori dake kusa da garin Bori, da misalin karfe 6 na safen yau, inda a ka kwashe kimanin bintina 30 a na harbe-harben.
A nashi jawabin Mai magana da yawun kwamitin ci gaban garin Kono/Boue Golden Nwibakpo ya karyata zargin cewa, al’umar garin ne keda alhakin kai harin.
Ko da aka tuntumi jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Rivers SP Nnamdi Omoni, ya yi alkawarin tuntubar wakilin Jaridar Daily Trust, domin yi mai bayani kan afkuwar lamarin.
Comments 1