Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Dakta Patrick Ifeanyi Ubah.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga ne suka kai wa ayarin motocin Sanatan hari a yammacin ranar Lahadi da kuma wasu mukarrabansa inda kuma aka hallaka wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Jihohi Da Su Mayar Da Dokar Kare Hakkin Nakasassu
A cikin rahoton, Ifeanyi Ubah ya tsallake rijiya da baya yayin da ‘yan bindigar suka kai wa tawagarsa hari a hanyar Enugwu-Ukwu a karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.
Da yake yin Allah wadai da harin, Soludo a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Mista Christian Aburime ya fitar, ya ce gwamnati ta kuduri aniyar kawar da duk wani laifi a jihar.
A cewarsa, “wannan shi ne yunkurin nutsewar jirgin ruwa na karshe” da wadannan gungun masu aikata laifuka suka yi”.
Ya kuma ba da tabbacin cewa a yanzu haka dukkanin hukumomin tsaro a jihar sun kasance cikin shirin ko ta kwana domin zakulo wadanda suka kai wannan mummunan harin.
Gwamnan ya kuma kara da cewa, za a sanya wadanda suka kai wa Sanatan hari su fuskanci fushin doka idan aka kama su.
Kazalika Gwamnan ya kuma jajantawa iyalan hadiman Sanatan da suka rasa rayukansu da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar, ga ‘yan sandan da su ma suka rasa rayukansu.
A wani labarin kuma, Wasu Shugabannin PDP Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC A Jihar Kogi
Wasu Jiga-jigan jam’iyyar PDP biyu a karamar hukumar Kogi, shugaban jam’iyyar mazaba da kuma tsohon mai ba da shawara na musamman, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karshen mako.
Shugabannin biyu da suka sauya sheka sune Muhammed Ozahi da Abdulkarim Shaibu Saikayi.