Gwamanatin jihar Kaduna ta jibge jami’an tsaro a titin filin tashi da saukar jiragen sama na jihar da nufin tabbatar da tsaro a jihar baki ɗaya.
Wannan na zuwa ne bayan kammala tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da jam’ian rundunonin tsaron ƙasar nan da jami’an hukumar lura da jiragen sama ta ƙasa da kuma shugabannin gargajiya, a ƙauyen Kutungare, dake yankin ƙaramar hukumar Igabi.
A jawabinsa lokacin taron tattaunawar gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufa’I, wanda kwamishinan tsaro da kuma lura da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya wakilta, ya buƙaci hakimai da dagatai da su bada haɗin kai domin tabbatar da tsaro a lokacin karɓar ta’aziyar marigayi sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
Baya da filin tashi da sauka, sauran wuraren da aka bada umarnin jibge jami’an tsaron sun haɗar da hanyar Birnin-Gwari da hanyar Kwalejin Horon jami’an soji da barikin Sojin Sama da wasu Unguwanni a jihar ta Kaduna.