A wani mataki na tallafawa al’umama sakamakon annobar Korona, gwamanatin tarayya ta fitar da jadawalin fara yin rijistar shirin rage raɗaɗi a yau litinin.
Cikin wata sanarwa da ofishin kula da ayyuka na tarayya ya fitar jiya lahadi a Abuja, ya ce, za’a buɗe shafin yin rijistar da misalin ƙarfe goma na daren yau litinin.
Ofishin kula da ayyukan na tarayya ya fitar da jadawalin waɗanda zasu yi rijistar zuwa kaso uku domin rage cunkosu a shafin ya yin yin rijistar a yau litinin.
A cikin jerin waɗanda za su amfana da shirin akwai masu neman tallafin kuɗaɗen makaranta da za su fara cikewa da misalin ƙarfe goma na dare yau.
Yayin da ‘yan-kasuwa masu manyan masana’antu kuma zasu fara cikewa a ranar juma’a ashirin da biyar ga watan nan da muke ciki na Satumba da misalin ƙarfe 12 na dare.
Har wa yau, za a ƙara buɗe shafin a ranar Litinin Ashirin da takwas ga watan nan, ga masu ƙananan sana’o’in dogaro da kai.
Haka kuma ofishin ya ce ga masu sha’awa da zarar an buɗe shafin za su iya yin rijista a shafin na yanar-gizo kamar haka:
www.survivalfund.ng.