An harbe wani mutum Oyinye Owunka ɗan shekaru a duniya har lahira sakamakon rikicin fili da ya ɓarke tsakanin mazauna yankin Obodogwugwu da Ugbolu dake ƙaramar hukumar Oshimili ta arewa a jihar Delta.
Jaridar Punch ta rawaito cewa an harbe mamacin ne a ranar Lahadin da ta gabata.
Wani wanda ya ganewa idonsa ya ce mamacin an harbe sa ne a yayin da rikici ya ɓarke kuma an zargin matasan yankin Ugbolu suka aikata wannan mummunan aiki.
“Akwai rikicin ƙasa da ake yi tsakanin yankunan biyu, kuma an kasa warware sa tsawon shekaru” inji sa.
“Shekaru huɗu da suka wuce mazauna yankin Ugbolu sun kai ƙara kotu akan filin amma daga ƙarshe basu yi nasara ba”.
Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Onome Onovwakpoyeya a ranar Litinin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an kashe mutum ɗaya akan rikicin fili, kuma ya zuwa yanzu dai babu wanda aka kama.