Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargadi da kakkausar murya, ga al’ummar Jihar cewar baza ta lamunci afkawa gine ginen mutane da sunan cin ganima ba.
Wannan gargadi kuwa ya haɗar da dukkan sassan jihar baki daya.
KU KARANTA: Cire Tallafin Fetur: Kuyiwa Allah Kada Ku Tafi Yajin Aiki, Ndume Ya Roki NLC
Haka kuma gwamnati na bayyana takaicin ta bisa yadda wasu Matasa suka afkawa ginin dake cikin tsohon gidan jaridar triump dake kusa da wapa.
Duk da cewa wannan ginin Ma baya cikin lissafin wuraren da Za’a rushe.
A saboda Haka gwamnati ta kara jadadda cewar duk Wanda aka Samu da laifin afkawa wani gini tare da kwashe kayayyakin jikin sa zai gamu da fushin hukuma.
Gwamnati ta kudiri aniyar yin aiki ne domin cigaban Jihar Kano Ba domin baiwa wasu lasisin rushe gine gine da sace kayan mutane babu gaira babu dalili ba.
Sakataren gwamnatin jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ne yayi wannan gargadi a madadin gwamnan, cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai, a yau Lahadi.
A wani labarin kuma: Za a Fara Kwashe Maniyyatan Kano A Yau Lahadi