Wata mata mai suna @shantellebelle, wacce ta ƙudiri aniyar cin ƙashin gashin kanta ta tattara kayanta ta koma gidanta duk da ba a kammala ginin sa ba.
A wani bidiyo da aka sanya a TikTok, matar ta nuna gadon da ta sanya a tsakiyar gidan domin ta riƙa barci. Ta bayyana cewa a haka kawai zata riƙa kwanciya a kansa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Batun dakatar da Opay da Palmpay, CBN ya bayyana gaskiyar zance
Ƴan ɗakiku cikin bidiyon kawai sai aka nuno ta akan gadon. Wasu bidiyoyin da ta ɗora a shafin nata sun nuna cewa ana ta cigaba da aiki a gidan bayan ta koma.
Lokacin da ta gayawa mutane cewa aikin yana ta kankama sosai, sun bayyana cewa nasarar da ta samu abin a taya ta murna ce.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon na ta ya yaɗu sosai inda aƙalla sama da mutum dubu ɗaya da ɗari biyu suka yi sharhi a kansa yayin da sama da mutum dubu ashirin suka danna masa alamar ‘like’.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@Mona Lisa ta rubuta:
“Yafi ace kana a inda ba a son ganin ka a wajen.”
@karizmento ya rubuta:
“Mama ban sanki ba amma na rantse ina alfahari dake.. ki cigaba da jajircewa.”
@Max Yeng ya rubuta:
“Ƴanmata ina alfahari da ke, babu abinda ya kai tsadar buri.”
@Heaven ya rubuta:
“Hangen nesan shine abinda yafi muhimmanci.”
Budurwa Ta Aika Saƙo Mai Sosa Zuciya Ga Budurwar Da Saurayinta Ya Rabu Da Ita a Dalilinta
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta aike da saƙo mai sosa zuciya kan budurwar da hankalin saurayin ta ya koma gare ta.
Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya ta aike da wani saƙo kan budurwar da ta yi mata ƙwacen saurayi.
Budurwar dai ta sanya wani bidiyo ne a manhajar TikTok, inda ta aike da saƙon ga budurwar da saurayinta ya rabu da ita a dalilin ta.