A ranar Talata ne gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2023 na Naira biliyan 148,958,122,525.05 ga majalissar dokokin jihar domin tantancewa tare da amincewa dashi.
Sule, a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin mai taken ‘Budget of Consolidation and Continuity’, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya da rikon amana da bin doka da oda domin ci gaban jihar baki daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Saudiyya Ta Ayyana Ranar Hutun Bayan Ta Lallasa Argentina A Gasar Cin Kofin Duniya
Ya ce, “Na yi farin cikin gabatar muku da jimillar kasafin kudin shekarar 2023 na Naira biliyan 148,958,122,525.05.
“Jimillar Naira biliyan 90,566,516,459.56 wanda ke wakiltar kashi 60.80 na jimillar kasafin kudin an ware shi ne domin kashe kudi akai-akai yayin da adadin Naira biliyan 58,391,606,065.49 wanda ke wakiltar kashi 39.20% na kasafin kudin an ware shi ne a matsayin kasafin kudi na shekara 2023.
“Kudirin kasafin kudin shekarar ta 2023 na bangarori daban-daban sune kamar haka:
Sashin Gudanarwar Gidan Gwamnati an ware masa – Naira biliyan 4.67, Tsaro / Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha – Naira biliyan 9.50, ban garen ‘yan majalissa an ware; Naira biliyan 2.00, Watsa Labarai/Al’adu da Yawon shakatawa; Naira Biliyan 2.71, Al’amuran Ma’aikata; Naira biliyan 1.41, Fansho; Naira biliyan 7.42.
“ban garen harkar noma da ruwan sha an ware ; Naira biliyan 11.32, Kudi, Ciniki da Zuba Jari; Naira biliyan 15.47, Bunkasa ababen more rayuwa; Naira biliyan 16.31, Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-kirkire; Naira biliyan 1.96.
“Ilimi; Naira biliyan 37.43, Lafiya; Naira biliyan 18.61, Ci gaban Matasa da Wasanni; Naira biliyan 3.04, Mata da Ci gaban Al’umma; Naira biliyan 1.02, Muhalli, Al’umma da Raya Karkara; Naira biliyan 10.25 da sauransu.
Gwamnan ya baiwa majalisar jihar da mazauna jihar tabbacin aiwatar da kasafin kudin, idan daga karshe ya zama doka.
Ya kuma bukaci ‘yan siyasa a jihar da su rika taka siyasa ba tare da dacin rai ba domin samar da zaman lafiya da ci gaba gabanin zaben 2023 mai zuwa.
“Bari na yi amfani da wannan damar na gabatar da kira ga ’yan’uwanmu da ke neman mukamai daga jam’iyyun siyasa daban-daban da su yi siyasa bisa ka’idar aiki domin zaman lafiya a Jihar Nasarawa yana amfanar kowa da kowa da kuma jama’a. rashin shi zai shafe mu baki daya,” Sule ya kara da cewa.
Da yake mayar da martani bayan karbar kasafin kudin 2023, kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Hon Ibrahim Balarabe-Abdullahi, ya yabawa Gwamna Sule bisa gabatar da kasafin kudin, ya kuma bada tabbacin shi da al’ummar jihar nan cikin gaggawa zasu tafiyar dashi domin samun ci gaba.
“Mai girma gwamna, ina so in lura da farin ciki, kyakkyawar alakar aiki da ta wanzu tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa tun lokacin da ka hau mulki a shekarar 2019.
“Ina kuma son in yaba muku bisa gyara da sanya kayan fasaha da aka yi a zauren majalisar da kuma gyaran zauren zartarwa da ofishin shugaban majalissa.” A cewar Rt.Hon Balarabe-Abdullahi.
A ranar 9 ga watan Disambar shekarar 2021, Gwamna Sule ya gabatar da kasafin kudin 2022 na Naira biliyan 109.8bn ga majalisar dokokin jihar wanda aka yiwa lakabin kasafin kudin canji mai dorewa.
A wani labarin kuma, Wani Dan Majalissar Dokokin Jihar Filato Ya Rasu
Wani Mamba mai wakiltar mazabar Qu’anpan ta Arewa a majalisar dokokin jihar Filato Eric Dakogol ya rasu.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin ya rasu ne a Jos, babban birnin jihar a ranar Litinin da yamma.