Sarkin Saudiyya Salman ya sanar da cewa za a gudanar da hutu a kasar a ranar Laraba bayan da tawagar kasar Saudiyya ta lallasa Argentina da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar 2022 a Qatar.
A cewar Arabnews, hutun ya biyo bayan Sarki Salman ya amince da shawarar da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya bayar na taya murnar nasarar da tawagar kasar ta samu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobe Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Takardun Kudin Naira — Emefiele
Dukkan ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da dalibai a kowane mataki na ilimi za a ba su hutu.
Saudiya ta yi murnar doke ‘yan Kudancin Amurka a wasan farko na rukunin C, inda suka tsayar da Lionel Messi da abokan wasansa, inda suka kawo karshen wasanni 36 da ‘yan Argentina suka yi ba tare da an doke su ba.
Larabawa sun sha yin rashin nasara a ko da yaushe a kan manyan kungiyoyin kwallon kafa tare da mafi wulakanci shi ne ci 8-0 da Jamus ta sha kashi a gasar cin kofin duniya na shekarar 2002 da aka gudanar a Koriya ta Kudu da Japan.
A wasan mai cike da tarihi da suka doke Argentina Saleh Alsheri ya rama kwallon a minti na 48 da fara wasa kafin daga bisani Salem Aldawseri ya zura kwallo ta biyu bayan mintuna biyar.
A ranar Asabar ne Saudiyya za ta kara da Poland ta Lewandowski.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Manchester United Ta Katse Kwantiragin Ronaldo, Zai Bar Kungiyar Nan Take
Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar fa katse Kwantiragin Cristiano Ronaldo wanda zai fara aikin nan take. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Bayanin hakan ya fito ne, a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafukanta na sada zumunta.