Wani matashi mai suna Ade ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi bayan ya yi sharhi kan hoton wata budurwa, LIB ta ruwaito.
Ya wallafa hakan ne a Facebook a wani rukuni ranar Talata, 22 ga watan Nuwamban 2022.
KU KARANTA: Yadda budurwa ta sharara wa saurayinta mari, ta ƙi amsar tayin aurensa, ta buƙaci ya zage damtsensa
Kamar yadda ya shaida, budurwarsa ta hassala ne bayan ganin sharhinsa karkashin bidiyon wata hakan yasa ta hukura da tarayya da shi.
A cewarsa, ba wani dogon sharhi yayi ba, kawai ce wa budurwar yayi ta yi kyau.
Da alama kishi ne ya sanya ran ta shi budurwar ya baci har ta yanke shawarar raba alaka.
Yadda Sule ɗan achaɓa ya cika bujensa da iska bayan budurwar da su ke lalata ta sheƙa lahira
Ana zargin Sule ya kebe da budurwa mai suna Muniat a ranar Juma’a da dare, amma kuma aka neme shi aka rasa bayan an ga gawarta a karamar hukumar Igbogbo Bayeku da ke Jihar Legas, Nigerian Pulse ta ruwaito.
An tattaro bayanai ka yadda mai kula da masaukin bakin ya duba dakuna kamar yadda ya saba inda ya tsinci gawar Muniat.
Bayan ganin hakan ne yasa mai kula da masaukin bakin yayi gaggawar sanar da caji ofis din Ikorodu, bayan nan ne jami’an ‘yan sanda su ka ci gaba da bincike.
A bayanin da yayi, kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya shaida cewa jami’ansu sun je wurin inda su ka tabbatar cewa babu wata alamar azabtarwa a jikin Muniat.