Wani Mamba mai wakiltar mazabar Qu’anpan ta Arewa a majalisar dokokin jihar Filato Eric Dakogol ya rasu.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin ya rasu ne a Jos, babban birnin jihar a ranar Litinin da yamma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobe Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Takardun Kudin Naira – Emefiele
Wata majiya daga iyalan mamacin da ta tabbatar wa wakilin Majiyar Dimokuradiyya faruwar lamarin ta ce dan majalisar ya yi rashin lafiya makonni kadan kafin rasuwarsa.
Da yake jajanta wa marigayin, gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan marigayin da kuma jihar baki daya, ya kara da cewa shi mai bin tafarkin dimokaradiyya ne na gaskiya kuma wakilin al’ummarsa.
Yace ” Eric ya kasance mai son al’umma, kuma ya jajirce wajen tunkarar kalubalen mazabarsa a ciki da wajen zauren majalisar kuma ya kasance yana daukar nauyin da goyan bayan dokokin da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar Al’ummar Jihar. ”
Wani labarin kuma, Ba Za Mu Kara Wa’adin Dena Amsan Tsofaffin Kudi Ba—Emefiele
Babban bankin Najeriya, CBN, Gwamna Godwin Emefiele, a ranar Talata ya dage kan cewa ba za a sauya wa’adin dena amfani da tsoffin takardun kudi na Naira ba.
Emefiele ya jaddada cewa, wa’adin zai kare ne a ranar 31 ga watan Junairu, 2023