Za a tura dalibai a jihar Ogun da suka aikata laifukan da suka sabawa doka zuwa gidajen kyaran halin na kananan yara domin a yi musu gyaran hali.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, na jihar Farfesa Abayomi Arigbabu, ne ya bayyana haka a Abeokuta lokacin da ya ziyarci kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Mista Lanre Bankole.
Arigbabu ya mika takardar neman afuwa a madadin gwamnatin jihar Ogun ga rundunar ‘yan sandan jihar, kan rashin da’a da wasu daliban makarantar Egba da kuma makarantar Asero da ke Abeokuta suka nuna.
A baya dai daliban sun ci zarafin babban jami’in yan sanda (DPO) dake kula da yankin Obantoko, na garin Abeokuta.
Kwamishinan ya bayyana harin a matsayin abin ban tsoro da ba za a amince da shi ba.
Ya Kuma gargadi daliban jihar da su kaurace wa aikata miyagun laifuka, yana mai cewa gwamnati ba za ta kara kare daliban ba, saboda shekarun su, amma ta za su fuskanci fushin doka.
Ya yaba da kokarin da ‘yan sanda suka yi na hada kai wajen kame dukkannin Dalibai masu munanan dabi’u a makarantu.
Arigbabu ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta magance duk wani nau’in rashin da’a ta hanyar sanya ido da mu’amala da dalibai da ‘yan sanda da jami’an gwamnati kan dawo da kyawawan halayen dalibai.
Da yake mayar da martani, Bankole ya bayyana cewa lamarin ya shafi ma’aikatar Ilimin jihar da ‘yan sanda, inda ya ce a ko da yaushe zai ci gaba da kasance mai himma a a kula da makarantu da ma jihar baki daya.
Idan za’a iya tunawa, Daliban makarantun biyu sun afkawa DPO da wasu jami’an ‘yan sanda a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da suke yunkurin dakile karya doka da daliban suka yi. Kamar yadda jaridar NAN ta ruwaito