Gwamnatin Tarayya Tayi Ƙarin Girma ga Jami’an Kashe Gobara 2,382
Hukumar Tsaro ta Civil Defence, Da Gyaran Ɗabi’a da Kashe Gobara,(CCFIB), ta amince da karin girma ga jami’an hukumar kashe gobara 2,382.
ACF Paul Abraham, kakakin hukumar ta Hukumar Kashe Gobara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
KARIN BAYANI:Zaben 2023: Ba Mu Rena Karsashin PDP, Da APC Ba, Amma Jam’iyar NNPP Zata Bada Mamaki—–Kwankwaso
A cewar sanarwar, Konturola Janar na Hukumar Kashe Gobara, Engr Jaji Abdulganiyu ne ya sanar da karin girma a cikin wata sanarwa daya fitar ta cikin gida.
Ya ce an kara wa jami’ai 363 karin girma yayin da 2,019 suka samu karin girma daga matsayin mataimakan Sufurtandanda na kashe gobara (ASF I) da mataimakin Sufurtandan kashe gobara (DSF) a shekarar 2022.
Jaji ya yabawa ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda shi ma ya zama shugaban hukumar, da sauran mambobi bisa irin rawar da suka taka wajen ƙara girman.
Ya taya daukacin sabbin jami’an da aka samu karin girma da kuma manyan jami’ai murna, sannan ya bukace su da su yi iya kokarinsu wajen tabbatar da cewa sun yi aiki akan wannan ƙarin girma da suka samu.
Jaji ya umurci shuwagabannin kwamandoji da sassan da su yi wa dukkan jami’an ado a cikin umarninsu da sassansu.
A WANI LABARIN: Masu Zanga-Zanga Sun Tsayar Da Al-amura Cak A Afrika Ta Kudu