A dai dai lokacin da ake samun tabarbarewar tattalin arziki da kuma hauhawar farashin kayayyaki a Afirka ta Kudu, dubban mutane sun shiga cikin wata sabuwar zanga-zangar da ta barke a kasar. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Babbar kungiya a daga cikin manyan kungiyoyin kwadagon kasar ne ke jagorantar yajin aikin, inda suka yi kira da a tsayar da al’amura cak a kasar, domin nuna adawa da karuwar rashin kayayyakkin masarufi, da tsadar man fetur da kuma karin kudi a bangaren wutar lantarki.
Ana sa ran gudanar da jerin gwano a dukkan garuruwan kasar, tare da yiwuwar gudanar da zanga-zangar a garuruwa masu girma da suka hada da Cape Town da Pretoria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kano Yayi Alƙawarin Samar Da Karin Jami’o’i Biyu A Jihar
Kungiyoyin dai na son gwamnati ta rage farashin man fetur, da kuma rage kudin ruwa da dai sahransu.
Rahotanni na nuna cewa, Kusan kashi uku na ‘yan Afirka ta Kudu ba su da aikin yi, kuma kasar na fuskantar matsin tattalin arzikin tun bayan barkewar annobar cutar Covid -19 da kuma mamayar Rasha a Ukraine.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa, masu shirya zanga-zangar a yau Laraba sun kuma bayyana cewa, suna da niyyar tsayar da al’umara cak a kasar
Sai dai anata bangaren, gwamnatin kasar ta Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, rashin biyan albashin da bata yi ba, ta dauki matakin ne bisa sabon tsarin da ta dauka na NO WORK NO PAY, a turance.
A gefe guda kuma kungiyoyin sun ce zanga-zangar na dya daga cikin matakan da suka fara dauka har sai sun cimma bukatun su.
A WANI LABARIN KUMA: Sojoji Sun Hallaka Yan Ta’addan Boko Haram 6 A Wani Luguden Wuta Da Su Kayi
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun runduna ta 21 na Amored Brigade dake garin Bama sun kashe mayakan Boko Haram guda shida a wani sumame da suka kai a wata haramtacciyar kasuwa da ‘yan ta’addan suka kafa a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
An rawaito cewa harin ya faru ne a yau Larabar da misalin karfe 11 na safe lokacin da sojojin tare da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (CJTF) suka kai farmaki kan haramtacciyar kasuwar da aka fi sani da Kasuwar Daula a kauyen Bararam a garin Bama.