A daidai lokacin da ake Jana’izar Marigayi Ibrahim Attahiru ne Hafsan Sojin Najeriya da ya rasa ransa sakamakon hatsarin Jirgin sama, lokacin kuma wasu gwamnoni suka dunguma zuwa wurin daurin auren dan Ministan Shari’a Abubakar Malami
Wannan ne ya sa yan Najeriya bayyana mabanbantar ra’ayoyi inda wasu ke ganin lallai Attahiru yayi mutuwar da ya gaza samun girmamawa daga wurin yan kasa, duk da cewa a bakin aiki ya rasa ran nasa.
Ko da yake ba wai ga gwamnonin ne kadai ba, hatta su ja gayya ja aiki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa ba su halarci jana’izar ba duk da cewa kowannen su na kasar.
To sai dai wata kila a iya cewa Kakakin Majalisar Dattijai Ahmad Lawan ya wakilce su domin yana wurin aka kammala komai.
Jim kadan bayan samun rasuwar Hafsan Sojin ne dai Malami ya sanar da dage aurwn dan nasa, to amma daga bisani an rada me ya faru kuma har aka daura auren a Masallacin Juma’a na Alfurqan dake birnin Kano
Daga Cikin gwamnonin da suka halarci taron daurin aure har Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da na Sokoto Aminu Tambuwal da Gombe Inuwa Yahaya da shi kan sa na Kano Abdullahi Umar Ganduje gami da gwamnan Kebbi Atiku Bagudu.