Mataimakin Gwamnan jihar Kwara Kayode Alabi ya bayyana cewa, wasanni da marasa ke yi na kawo takaita aikukan ta’addanci.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da Babban Maitaikawa Mataimakin Gwamnan a kan kafofin yada labarai, Modupe Joel ya fitar a jiya juma’a,, Wanda sanarwar ke dauke da taken “Mataimakin Gwamnan jihar Kwara ya dukufa wurin cigaban Matasa”.
A cewar sanarwa Alabi ya yi kira ga Matasan da su shiga cikin fannin wasannin ne, lokacin da ya ke jawabi a wurin rufe gasar wasanni na Igbaja da ya gudana a Makarantar Sakandare ta ECWA dake garin Igbaja na karamar hukumar Ifelodun a jihar.
Kazalika sanarwar ta ce”Mr Alabi ya karfafawa Matasan gwuiwa wajan jajircewa, da kuma nuna da’a, inda ya ce, harkan wasanni ya daga darajen wasu mutane da dama, kuma ya na hada kan al’uma batare da nuna babban cin addini ko kabilanci ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: PSG ta sabunta wa Kocin ta kwantiragi
“Harkan wasanni na taimaka wa Matasa wurin bunkasa yankin su, da kuma inganta rayuwar su, inda kuma ya kara da cewa, hakan zai raimaka wajan rage adadin samun laifukan ta’addanci” inji shi.
Shi ma wani Uba a yankin na Igbaja Alhaji Dakta Abdulraheem Amoo Oladimeji ya yaba wa gwamnatin jihar, bisa irin kokarin da ta ke yi wurin karfafa wa matasan jihar, ta hanyar shirye-shirye da zai amfane su.
Daga cikin mahalarta taron a kwai Honorabul Raphael Adetiba Shugaban majalissar dokokin jihar ta Kwara, wanda ya jadda cewa, matasa su ne kashin bayan cigaban kowace yanki.
Comments 1